Allah Ya yiwa Sabuwa ta shirin Daɗin Kowa rasuwa
Allah Ya yiwa Sabuwa ta shirin Daɗin Kowa rasuwa
Allah ya yi wa Hajiya Halimatus Sadiya wacce aka fi sani da Sabuwa a shirin Dadin Kowa na tashar Arewa24 rasuwa.
Arewa Updates ta rawaito cewa, ‘yarta Amina wadda aka fi sani da Raliya ‘yar Bijilanti a shirin Dadin Kowa ce ta tabbatar da Arewa Updates rasuwar.
Za a yi janaʼizarta da safiyar Ahamis 19 ga Maris 2026 a gidanta da ke unguwar Dan Maliki, daura da gidan Man Danlami a Karamar Hukumar Kumbotso.
Ku kuma karanta: Iran ta tabbatar da mutuwar shugaban tsaron ƙasar, Ali Larijani
Marigayiyar gogaggiyar jaruma ce a masana’antar Kannywood, inda ta shafe sama da shekaru 20 tana fitowa a fina-finai daban-daban kafin ta shiga shirin Dadin Kowa.
Marigayiyar ta yi fice a shirin Daɗin Kowa mai dogon zango, a matsayin Sabuwa, matar Malam Ayuba mai gadi kuma mahaifiyar Ɗan Asabe, inda aka san ta da haƙuri, hikima da kuma kishin tarbiyyar iyali, halayen da suka sa masu kallo suka daɗe suna ƙaunarta.
A baya ta taɓa kokawa kan matsalolin ƙangin rayuwa, abin da ya janyo cece-kuce a masanaʼantar.
Shirin Dadin Kowa na tashar AREWA24 na daga cikin fitattun shirye-shiryen fina-finan Hausa da suka samu karɓuwa sosai, inda ya taɓa lashe lambar yabo a matsayin mafi fice a gasar AMVCA.









