Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta yi kira ga al’umma da su yi taka tsantsan da saka ido a bukukuwan Sallah
Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta yi kira ga al’umma da su yi taka tsantsan da saka ido a bukukuwan Sallah
Rundunar ‘Yansandan jihar Yobe tana miƙa saƙon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Maiduguri ta jihar Borno bisa mummunan harin fashewar bama-bamai da ya faru a ranar 16 ga Maris, 2026 da misalin karfe 1830 na yamma a wurare daban-daban a cikin Maiduguri.
Rundunar tana kira ga al’ummar Jihar Yobe da su kwantar da hankulansu tare da kara tsananta lura da tsaro, musamman a cikin unguwanni, wuraren taruwar jama’a da sauran wuraren da ake yawan zirga-zirga.
A wata takarda da kakakin rundunar ‘yansandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim ya fitar, ta ce biyo bayan taron Majalisar tsaron jihar da aka gudanar a Yobe State Government House a ranar 16 ga Maris, 2026, tare da dukkan hukumomin tsaro a jihar, an tsara ingantattun matakan tsaro a fadin jihar domin tabbatar da zaman lafiya kafin, lokacin, da bayan bukukuwan Sallah.
Kwamishinan ‘Yan Sanda, Emmanuel Ado, psc, fdc, ya umarci Area Commanders, DPOs, sassan rundunonin musamman da sashen leƙen asiri da su tabbatar da samar da ingantaccen tsaro a masallatai, wuraren shakatawa, filayen wasa da sauran muhimman wurare kafin, yayin da kuma bayan bukukuwan Sallah.
Rundunar tana kira ga al’umma da su hada kai da hukumomin tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai kan duk wani mutum, abu, mota ko babur da ake zargi, ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
Haka kuma ana gargadin masu ababen hawa da su guji tukin ganganci ko tukin da zai iya jefa rayuwar jama’a cikin hadari a wannan lokacin bukukuwa.
Rundunar ta kuma lura da takaici yadda a wasu bukukuwan da suka gabata wasu matasa ke rike da makamai ko wasu abubuwa masu hadari yayin murnar Sallah. Wannan dabi’a ba za a amince da ita ba, kuma duk wanda aka samu da makami ko wani abu mai hadari za a dauki matakin doka a kansa ba tare da bata lokaci ba.
Haka kuma ana shawartar al’ummomi da su karfafa tsarin sa-ido na unguwanni (neighbourhood watch) domin daukar matakan kariya tun da wuri.
Tsaro hakkin kowa ne. Idan ka ga wani abu mai ban tsoro, ka sanar da hukuma.









