Shugaba Tinubu, ya shawarci ‘yan Najeriya da su sanya idanu kan yadda gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi ke kashe kuɗaɗe
Shugaba Tinubu, ya shawarci ‘yan Najeriya da su sanya idanu kan yadda gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi ke kashe kuɗaɗe
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci kafafen yada labarai su rika sanya ido ga jihohi da kananan hukumomi kan yadda suke amfani da kudaden da suke karba daga gwamnatin tarayya.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin wani taron buda baki na addinai daban-daban da masu gidajen jaridu da shugabannin kafafen yada labarai a fadar gwamnati da ke Aso Rock Presidential Villa, a Abuja.
Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar, musamman cire tallafin man fetur, sun kara yawan kudaden da jihohi ke samu. Ya kara da cewa yanzu kananan hukumomi ma na samun kudinsu kai tsaye.
Tinubu ya kuma ce a halin yanzu babu wata jiha da ke karbar bashi domin biyan albashin ma’aikata, yana mai jaddada cewa dole ne a sarrafa abin da ake da shi domin ci gaba da tafiyar da kasa.
Haka kuma ya yabawa kafafen yada labarai kan sukar gwamnatinsa, yana mai cewa hakan na taimaka masa wajen kara himma da inganta shugabanci domin amfanin al’ummar Najeriya.









