Idan ma Netanyahu bai mutu yanzu ba to nan gaba kaɗan za mu hallaka shi – Iran
Idan ma Netanyahu bai mutu yanzu ba to nan gaba kaɗan za mu hallaka shi – Iran
Rundunar Sojojin Juyin-Juya-hali ta Iran (IRGC) ta ci alwashin hallaka Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.
Daily Trust ta rawaito cewa a wani sako da ta wallafa a shafin ta na yanar gizo mai suna Sepah News, IRGC idan ma Netanyahu, wanda ta kira da “azzalumi makashin ƙananan yara” ya na raye a halin yanzu, to ba makawa za ta ci gaba da fakon shi har sai ta hallaka shi da ƙarfin tuwo.
Hakan na zuwa ne yayin da jita-jita ta ke ƙara ƙarfi cewa an kashe Netanyahu a hare-haren da Iran din ke kai wa Isra’ila.
Tun a karshen mako jita-jitar ke ta yaɗuwa, duk da cewa Ma’aikatar Tsaro ta Isra’ila (IDF) ta ƙaryata raɗe-raɗin.









